Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-zangar Matasa Ta Rikide Zuwa Rikici | World Briefings
Subscribe to World Briefings's newsletter

News Updates

Let's join our newsletter!

Do not worry we don't spam!

World

Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-zangar Matasa Ta Rikide Zuwa Rikici

1 August, 2024 - 8:05PM
Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-zangar Matasa Ta Rikide Zuwa Rikici
Credit: solacebase.com

Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-zangar Matasa Ta Rikide Zuwa Rikici

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da ƙaƙaba dokar hana fita a jihar bayan zanga-zangar nuna fushi kan matsin rayuwa ta rikiɗe zuwa rikici.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wani taron manema labaru da ya gudanar yau a Kano.

Zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tarzoma ne bayan wasu matasa sun fara afka wa wuraren ajiye abinci suna wawashewa. Hakan ya haifar da arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro.

Taron Gaggawa

A cikin bayanin nasa, gwamnan na Kano, Abba Kabir ya ce: "A taron tsaro na gaggawa da muka gudanar da shugabannin hukumomin tsaro a jihar Kano, gaba ɗayanmu mun yanke shawarar ƙaƙaba dokar hana fita ta awa 24 domin ganin an dawo da doka da oda."

Wasu daga cikin masu zanga-zanga sun ɓalle wuraren ajiye kayan abinci, inda suka kwashe buhunan shinkafa, kwalayen taliya da kuma man girki. A ranar Laraba Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nemi masu zanga-zangar da su guji tashin hankali, har ma ya gayyace su zuwa gidan gwamnati domin kai ƙorafinsu.

Kira ga Gwamnati

"Ina tabbatar muku cewa gwamnati ba za ta lamunci irin waɗannan ayyukan ba," in ji shi yayin da yake yi wa ƴan kasuwa da sarakunan gargajiya, da malaman addini jawabi a gidan gwamnati. "Maimakon haka, ina miƙa goron gayyata ga masu son yin zanga-zanga da su zo gidan gwamnati, inda zan ji daɗin sauraren koke-kokensu kuma mu gudanar da tattaunawa mai ma’ana."

Titin zuwa gidan gwamnatin Kano da aka fi sani da State Road, shi ne wuri na farko-farko da ya fara shaida fushin matasan, inda suka farfasa duk abubuwan da suka gani a gefen titin. Wasu masu zanga-zangar sun fasa wani shagon sayar da kaya tare da yashe kayayyakin da ke cikinsa. Sai dai ‘yansanda sun harba musu hayaƙi mai sa hawaye.

Bayanai Daga Wurin Lamarin

"Duk wanda ya san wannan titi ya sani cewa a tsare yake amma yanzu an yamutsa wurin gaba ɗaya," in ji wakilin BBC a Kano Zahraddeen Lawan. A gefe guda kuma, ‘yansanda sun bi sun ƙwato wasu daga cikin kayayyakin da aka kwashe kuma suka tara su wuri guda.

Kazalika, matasan sun auka wa katafaren ginin nan na Digital Industrial Park da ke cikin sakatariyar Audu Bako. Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta gina shi da zimmar horar da matasa game da harkokin sadarwa da kuma ƙirƙirarriyar fasaha. Rahotonni na cewa a mako mai zuwa ne ake sa ran ƙaddamar da shi.

Hotouna da bidiyo da aka wallafa a shafukan zumunta sun nuna yadda ɓata-garin suka dinga saran ƙofar ginin da makamai, yayin da wasu rahotonni ke cewa an cinna wa wani ɓangare na ginin wuta. Ana iya jin ƙarar wani abu da ya yi kama da harbin bindiga, amma duk da haka ba su fasa yunƙurin shiga cikin ginin ba. A gefe guda kuma, wasu na ta yunƙurin tumɓuke turaku da wayoyin da aka kakkafa a tsakiyar titin na State Road.

Gwamnan Ya Karɓi Jagororin Masu Zanga-zanga

Kamar yadda ya yi alƙawari Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya karɓi jagororin wasu ƙungiyoyi da ke zanga-zangar a gidan gwamnatinsa da ke ƙwaryar birnin. Yayin ganawar tasu, ƙungiyoyin sun gabatar masa da ƙorafe-ƙorafensu a rubuce domin ya isar da su ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

Sai dai gwamnan ya zargi wasu da ya bayyana da "marasa kishin Kano" da ɗebo 'yandaba domin shiga cikin zanga-zangar. "Sai aka samu wasu marasa kishin Kano sun shgo mana ‘yandaba. Tun jiya muke faɗar inda suke amma sai suka ɓoye su," a cewar gwamnan. "Yau [Alhamis] da safe aka dinga ɗebo su a mota ana kawo su shataletale, suka hana waɗannan ƙungiyoyi nagartattu masu kishi zuwa su ba da takardu."

Haka nan, gwamnan ya yaba wa jami’an tsaro game da "matuƙar ƙoƙarin tarwatsa su".

© 2024 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Roki Gwamnatin Tarayya

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya roki gwamnatin tarayya da ta gaggauta rage farashin man fetur da kudin wutar lantarki.

Gwamnan ya yi rikon ne a ranar Laraba yayin ganawa da Malamai da Sarakuna da ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a yayin da ake shirin fara zanga-zanga. Acewar Gwamnan, tsadar man fetur da karin kudin wutar lantarki ya haifar da damuwa ga ‘yan Najeriya wanda hakan yasa suke shirin fita zanga-zanga.

"Yakamata gwamnati ta duba karin kudin wuta da aka yi. Wani karin matsala ne ga ‘yan Najeriya. Muna kira ga gwamnatin tarayya ta rage farashin wanda hakan zai saukakawa ‘yan Najeriya”, inji shi.

Game da zanga zangar kuma, Gwamna Abba ya bayyana cewa duk da cewa doka ta bada damar a yin zanga-zanga amma dole ne ta zama ta lumana. Sannan ya ce bazai je ko ina ba, zai tsaya ya tarbi masu zanga zangar tare da mika kokensu ga shugaban ƙasa.

Rikicin Zanga-zangar Ya Ƙaraɗe Kano

Kano - Rahotanni sun bayyana cewa an kashe wani mai suna Ismael Ahmad Musa a yankin Hotoro da ke karamar hukumar Tarauni a jihar Kano. An ce wanda aka kashen mazaunin Hoto Danmarke ne, kuma dan uwansa Mubarak ne ya tabbatar da mutuwarsa a ranar Alhamis. Masu zanga zanga sun ci karfin jami'an tsaro, an toshe babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna. Jaridar Daily Trust ta ce har yanzu ba a gano ko Ismael na daga cikin matasan da ke zanga-zangar yuwa ko kawai dan ba ruwana ne. Tuni dai aka ce an yi wa mamacin sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Baya ga Ismael an ce akwai kuma wani matashi da ya samu mummunan rauni wanda aka garzaya da shi asibitin Aminu Kano (AKTH) domin ceto rayuwarsa. Ana zargin cewa harsashin bindiga ne ya same shi. A hannu daya kuma, kamfanin dillancin labaran NAN ya ruwaito cewa an cinnawa ofishin hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) na Kano wuta. NAN ta ce wasu gungun matasa ne wadanda ke dauke da makamai suka cinnawa ofishin wuta inda kuma suka mamaye manyan titunan Kano. An ce mako mai zuwa ne aka shirya kaddamar da sabon ofishin kafin wannan ta'

A yankin Hotoro da ke Kano, rahotanni sun ce an rufe shaguna yayin da aka bankawa wani gidan mai da kuma shagon Rufaida wuta, inji rahoton Premium Times. Wasu mazauna yankin sun yi kira ga jami'an tsaro da su gaggauta daukar matakai domin dawo da zaman lafiya da kuma kare dukiyoyin al'ummar jihar. A wani labarin, mun ruwaito cewa daruruwan masu zanga-zanga sun rufe babbar hanyar da ke kai mutum jihar Kaduna daga birnin tarayya Abuja. Rahotanni sun bayyana cewa saboda yawan matasan, 'yan sandan da ke wajen sun gagara yin komai kan wannan cunkuson ababen hawa da toshe hanyar ya haifar.

Gwamnatin Kaduna Ta Sanya Dokar Hana Fita?

Kaduna - Wani rahoto da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna cewa gwamnatin Kaduna ta sanya dokar hana fita ta awanni 24 sakamakon zanga-zanga. An ce gwamnatin ta sanya dokar ne biyo bayan kona kadarorin gwamnati da satar dukiyar jama'a da 'yan daba suka rika yi ana tsaka da yin gangamin. Sai dai Gwamna Uba Sani ya karyata wannan rahoto, inda ya wallafa a shafin gwamnan jihar na Facebook cewa gwamnatin Kaduna ba ta sanya dokar ta baci ba tukunna. A ranar Alhamis, Gwamna Uba Sani ya ce tuni gwamnati da jami'an tsaro a jihar suka shawo kan tashin hankalin da ke faruwa a sassan jihar. Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu 'yan daba da suka saje da masu zanga-zanga sun kai farmaki ofishin hukumar KASTLEA inda suka cinnawa ginin wuta. An ce bayan kona wani bangare na ginin, 'yan daban sun kuma wawushe wasu kayayyaki da aka ajiye a ciki, inda daga bisani suka fasa gidaje da shagunan jama'a. A hannu daya kuma, jami'an 'yan sandan sun fara harbi kan masu zanga-zanga a wasu sassa na jihar Kaduna domin kwantar da tarzoma. A wani labarin, mun ruwaito cewa zuwa yanzu jihohin Arewa uku ne aka sanya dokar hana fita ta awanni 24 bayan fashewar bam da kuma munanar zanga-zanga. Yayin da jihohin Kano da Yobe suka sanya dokar hana fita saboda tashin hankula da aka samu sanadin zanga-zanga, an ce gwamnatin Borno ta sanya dokar ne bayan fashewar bam.

ECOWAS Ta Yi Kira ga Kasashen Nijar da Benin

FCT, Abuja - Kungiyar ECOWAS ta bukaci kasashen Nijar da Benin su koma teburin sulhu domin bude iyakokinsu. Shugaban harkar kasuwanci a kungiyar ECOWAS, Dakta Muhammad Chambas ne ya yi kiran a Abuja. Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Dakta Muhammad Chambas ya bayyana amfanin da za a samu idan kasashen suka bude iyakokinsu. Rahotanni sun nuna cewa tun a watan Yulin shekarar 2023 aka rufe iyakokin kasashen Nijar da Benin saboda wani sabani da suka samu a tsakaninsu. A shekarun baya kasashen sun kasance suna ƙawance ta bangarori da dama kuma ana harkokin kasuwanci da tafiye tafiye ta iyakokinsu. Dakta Muhammad Chambas ya bayyana cewa idan aka bude iyakokin za a samu sauƙin zirga zirga a tsakaninsu. Muhammad Chambas ya kara da cewa za a samu sauki a harkar kasuwancin ƙasashen da sauran ƙasashen da ke makwabtaka da su. Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Dakta Muhammad Chambas ya yi kira ga shugaban Nijar da Benin kan sake zama domin duba bude iyakokin kasashen. Chambas ya ce ya kamata Nijar da Benin su duba 'yan uwantaka na Afirka da ECOWAS da ya hada su wajen yin gaggawar bude iyakokin.

Masu Zanga-zangar Sun Kunna Wuta A Kofar Gidan Gwamnati

Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da wahalhalun da ake fama da su a fadin kasar nan sun kunna wuta a kofar gidan gwamnati da ke Kano a safiyar ranar Alhamis. Masu zanga-zangar daga sassa daban-daban na birnin sun yi dandazo ne a gidan gwamnati, inda gwamna Abba Kabir Yusuf zai yi musu jawabi. Sai dai wasu daga cikinsu sun hada tayoyi suka banka musu wuta a lokacin da suke tunkarar kofar gidan gwamnatin. Hakan ya sanya jami’an tsaro a gidan gwamnati suka harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar. Masu zanga-zangar sun tsere inda suka nufi hanya daban-daban cikin rudani.

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-zangar Matasa Ta Rikide Zuwa Rikici
Credit: leadership.ng
Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-zangar Matasa Ta Rikide Zuwa Rikici
Credit: punchng.com
Tags:
Zanga-zanga Kano curfew Kano dokar hana fita zanga-zanga rikici
Luca Rossi
Luca Rossi

Environmental Reporter

Reporting on environmental issues and sustainability.